Channel Avatar

ILIMIN TAFIN HANNU TV CHANNEL @UCtFDTBuz0dnQllxyIJWEPHQ@youtube.com

16K subscribers

Duniyar Ilimin Tafin Hannu ( Palmistry ) +2347016333007 Tha

Welcoem to posts!!

in the future - u will be able to do some more stuff here,,,!! like pat catgirl- i mean um yeah... for now u can only see others's posts :c

ILIMIN TAFIN HANNU TV CHANNEL
Posted 1 month ago

MASU HIKIMA SUNCE

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Idan kana son ganin yadda duniya za ta kasance a bayanka ka duba yadda take a bayan mutuwar wani irinka. Za ka ga yadda masoya ke manta masoyansu, rigima ta harde tsakanin magadansu. Wanda bai manta ka kawai shi ne Allah mahaliccinka. Manta da kowa ka nemi yardarSa.

*
*

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Wanda ba ya sallah an haramta ma sa dadin duniya, kuma zai gamu da wahalhalu a wurare guda hudu: A nan duniya, da ranar mutuwa, da cikin kabari da ranar hisabi. A nan duniya ana debe ma sa albarka, a cire ma sa kwarjini daga fuska, a sa ma jama'a kyamar sa. A ranar mutuwa zai mutu da wulakanci da yunwa da kishirwa. A cikin kabari Allah zai kuntata ma sa, a hasa ma sa wuta a cikin kabarinsa, a aika ma sa kumarci a tsakanin fatar jikinsa da namansa. A ranar hisabi za a bakanta fuskarsa, a yi masa hisabi dalla dalla, sannan a hada shi da zabaniyawa da za su wurga shi cikin wuta. Ya kai dan uwa mai sallah ka gode ma Allah a kan ni'imar da kake cikin ta da wadda za ka shiga a cikin ta bayan mutuwarka.

*
*
๐Ÿ‘‰๐Ÿป Idan duniya ta aure ka sai ta kwashe alherin mutane ta yaba ma ka. Idan kuwa ta sake ka sai ta kwashe alheranka ta jefa ma wasu.

*
*

Yaษ—a bayani daga naku:- khalifson

5 - 0

ILIMIN TAFIN HANNU TV CHANNEL
Posted 1 month ago

*WASIYYOYI* *GUDA 5 DAGA* *MANZON
ALLAH*
*(S.A.W).*
Manzon Allah (s.a.w) yace: "Waye zai karbi
wadannan Kalmomi
guda 5 daga gareni, yayi Amfani da su, ko ya
Sanar
da wanda zai yi Amfani da su"
Sai Abu Huraira (R.A) yace Ni Zan karba ya
Ma'aikin
Allah.
Sai Manzon Allah (s.a.w) ya rike Hannu na
yace min:-
1. Ka guji Aikata Sabo, Zaka Zamo wanda yafi
kowa Bauta a cikin Mutane.
2. Ka yarda da Abinda Allah Ya baka, Zaka fi
Kowa
Arziki Cikin Mutane.
3. Ka kyautata wa Makobcin ka, Zaka Zamo
(cikakken) Mumini.
4. Ka So Wa Mutane Abinda Kake So Wa
Kanka, Zaka Kasance (cikakken) Musulmi.
5. Kada ka Yawaita Dariya, Domin Yawan
Dariya na
Kashe Zuciya.
"Manzon Allah (S.A.W) Yace Ka Rike su Ko ka
Sanar da Wanda Zaiyi Amfani
Dasu".
Idan ka Tura Wa 'Yan Uwa Musulmai Baka
San Wa Zaiyi
Amfani Dasu Ba, Kaga Ka Samu Ladan
Mutane Masu Tarin
Yawa.
Ubangiji Allah ya bamu ikon aikatawa

7 - 0

ILIMIN TAFIN HANNU TV CHANNEL
Posted 1 month ago

Ina Gaiyata Ku Wajan Daurin Aure Na

4 - 0

ILIMIN TAFIN HANNU TV CHANNEL
Posted 1 month ago

MASU HIKIMA SUNCE:

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Abubuwa uku idan sun tafi ba su dawowa:
1. *Magana*
2. *Lokaci*
3. *Mutunci.*

๐Ÿ‘‰๐Ÿป A da can mutane ba su da asibitoci amma su na da lafiya. Ba su da yawan kudi amma su na da arziki. Ba yawan makarantu amma akwai ilimi. Ba hanyoyin sufuri da na sadarwa amma akwai sada zumunta. Ba su da yawan ni'imomi amma su na da jin dadi. Ko ka san dalili?
"Albarkar abu ta fi yawansa".

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Babbar alamar girman kai ita ce ka raina mutane ko ka ki karbar gaskiya. Mutakabbiri bai shiga aljanna.

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Ba kowace faduwa ce matsala ba. Da yawa wanda zai fadi amma idan ya tashi ya sheqa ba ka iya cim ma sa.

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Kada ka cuci wanda ya cuce ka. Sharri Kare ne ko ya yi nisa zai dawo ma mai shi.

*Rubutawa Bayani Daga Naku:- Umar Faruk AkA โ€œkhalifsonโ€

5 - 0

ILIMIN TAFIN HANNU TV CHANNEL
Posted 1 month ago

MASU HIKIMA SUNCE:

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Idan ba ka son a soke ka kada ka ce komai, kada ka aikata komai. Duk wanda ya motsa dole ne sai an soke shi.

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Mafi hankalin mutane shi ne wanda ya bar duniya kafin ta bar shi, ya gyara kabarinsa kafin ya shige shi, ya yi sallah a cikin jama'a kafin su sallace shi, sannan ya yi ma kansa hisabi kafin a gurfanar da shi a ranar hisabi.

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Ba ka sanin dadin lafiya sai idan ciwo ya zo. Ba za ka san dadin zaman lafiya ba sai ka gamu da tashin hankali. Ana sanin dadin haduwa ne idan an rabu. Gode ma ni'imomin Allah wadanda ka sani da wadanda ba ka sani ba.

๐Ÿ‘‰๐Ÿป (Matsalolinmu a yau guda biyu ne: Mu yi aiki kafin mu yi nazari, ko mu yi ta nazari ba aiki.)
*
๐Ÿ‘‰๐Ÿป( Idan ka taimaki wani saboda Allah kada ka jira ya yi maka godiya. Falalar Allah da yardarSa sun fi amincewa da yardar mutane.)
*
๐Ÿ‘‰๐Ÿป (Yana da kyau ka damu da damuwar dan uwanka. Abin da ya fi wannan shi ne ka taimaka ma sa domin ya fita damuwa.)
*
๐Ÿ‘‰๐Ÿป( Kyau iri uku ne: Akwai kyan jiki, akwai kyan hali, akwai na zuciya. Kyan zuciya shi ke sada ka da Allah. Kyan hali yana sada ka da mutane. Kyan jiki kuwa a kullum sai ya ja ma ka fitina. Duba tarihin Annabi Yusuf.)
*
๐Ÿ‘‰๐Ÿป (Abinda ka koya da farko a cikin addini shi ne abinda za a tambaye ka a cikin kabarinka. Ba tarin ilimi ke da muhimmanci ba. Amfanin ilimi aiki da shi.)
*
๐Ÿ‘‰๐Ÿป (Magana tsuntsu ce. Idan ta fita ba a iya kamo ta. Ka iya bakinka ko ka kwana cikin nadama.)

AkA Khalifson

6 - 0

ILIMIN TAFIN HANNU TV CHANNEL
Posted 2 months ago

MASU HIKIMA SUNCE:

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Idan ba ka son a soke ka kada ka ce komai, kada ka aikata komai. Duk wanda ya motsa dole ne sai an soke shi.

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Mafi hankalin mutane shi ne wanda ya bar duniya kafin ta bar shi, ya gyara kabarinsa kafin ya shige shi, ya yi sallah a cikin jama'a kafin su sallace shi, sannan ya yi ma kansa hisabi kafin a gurfanar da shi a ranar hisabi.

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Ba ka sanin dadin lafiya sai idan ciwo ya zo. Ba za ka san dadin zaman lafiya ba sai ka gamu da tashin hankali. Ana sanin dadin haduwa ne idan an rabu. Gode ma ni'imomin Allah wadanda ka sani da wadanda ba ka sani ba.

*(khalifson)*

4 - 0

ILIMIN TAFIN HANNU TV CHANNEL
Posted 2 months ago

Virgo (Subulatu Turabin 6 โ€“ daga 23 ga Agusta zuwa 22 ga Satumba):

๐ŸŒฟ Asalin Virgo

Taurari: Virgo yana cikin Earth signs (tare da Taurus da Capricorn).

Sarrafawa: Mercury โ€“ tauraron tunani da sadarwa.
Sabiโ€™a: Mai hankali, mai natsuwa, mai son tsari da tsafta.

๐Ÿง  Halin Zuci da Tunani

Virgo mutum ne mai nazari da lura sosai.
Yana son tsari da yin abubuwa a cikin daidaito.
Mai kula da kananan abubuwa (detail-oriented).
Wani lokaci yana iya zama mai yawan damuwa saboda tunani.

๐Ÿ’ช Dabiโ€™a da Sabiโ€™a

Mai son tsafta, tsari da kyakkyawan yanayi.
Mai aiki tukuru kuma yana son ganin sakamako mai kyau.
Mai taimako, yana iya kula da mutane cikin gaskiya.
Amma wani lokaci yana iya zama mai yawan sukar mutane saboda tsananin lura da gyara.

โค๏ธ Soyayya da Zamantakewa

Virgo mutum ne mai aminci a soyayya.
Ba ya son yin wasa da zuciya โ€“ yana shiga soyayya da hankali.
Mai son nuna soyayya ta hanyar taimako da kulawa, ba lallai da kalmomi kawai ba.
Amma wani lokaci yana iya zama mai yawan tambaya ko bincike a soyayya.

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง Aure da Iyali

A aure, Virgo yana da gaskiya da amana.
Yana son a yi rayuwa cikin tsari da tsafta.
A matsayin uba/uwa, yana koya wa โ€™yaโ€™yansa tsari, aiki tukuru da gaskiya.
Amma yana iya zama mai tsauri sosai idan abubuwa ba su tafi daidai ba.

๐Ÿ’ผ Aiki da Kasuwanci

Ya dace da aikin da ke bukatar tsari, hankali da lura da cikakkun bayanai.
Yana iya yin kyau a aikin lafiya (likitanci, jinya), rubuce-rubuce, bincike, kasuwanci mai tsari.
Ba ya son sakaci ko wasa da aiki.

๐Ÿ˜‡ Karfi da Rauni

Karfi: Hankali, tsari, tsafta, aminci, aiki tukuru.
Rauni: Yawan damuwa, yawan sukar mutane, iya zama mai tsauri, rashin sassauci.

๐Ÿ‘จโ€๐Ÿฆฐ Namiji Virgo

Mai hankali, mai tsari, mai gaskiya.
Yana son mace mai tsafta da nutsuwa.
A soyayya yana nuna kauna ta ayyuka da taimako.
Amma yana iya zama mai tsauri idan ba a yi abubuwa daidai ba.

๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿฆฑ Mace Virgo

Mai tsafta da natsuwa.
Mai kulawa da mutane da taimako.
A soyayya tana da gaskiya da amana.
Amma tana iya zama mai yawan bincike ko tambaya ga saurayinta.

๐ŸŒŸ A takaice, Virgo mutum ne mai hankali, tsari da tsafta, mai aminci amma yana bukatar ya rage yawan damuwa da sukar mutane.

By khalifson

5 - 0

ILIMIN TAFIN HANNU TV CHANNEL
Posted 2 months ago

BAYANI AKAN ILIMIN FALAKI.โญ

ุงู‚ุณุงู… ุนู„ู… ุงู„ูู„ูƒ
Wato rarrabewar ilimin falaki.
Domin shi ilimin falaki takasu ne. Gida uku. 3.
Gasunan kamar haka.๐Ÿ‘‡
1-ilmul taqwim. ุนู„ู… ุงู„ุชู‚ูˆูŠู…
2-ilmul hai'at. ุนู„ู… ุงู„ู‡ูŠุนุฉ
3-ilmul tanjim. ุนู„ู… ุงู„ุชู†ุฌูŠู…

ilmul taqwim. Shine ilimin da ake sanin tafiyar taurari.
Saurinsu da juyawarsu.
Da wannan iliminne ake sanin adadin shekaru.
Da shine ake rubuta kalanda (calendar)โœ๏ธ

ู‚ุงู„ ุงู„ู„ู‡ ุชุนุงู„ู‰ุŒ
ู‡ูˆ ุงู„ุฐูŠ ุฌุนู„ ุงู„ุดู…ุณ ุถูŠุงุกูˆุงู„ู‚ู…ุฑ ู†ูˆุฑุง ูˆู‚ุฏุฑู‡ ู…ู†ุงุฒู„ ู„ุชุนู„ู…ูˆุงุนุฏุฏุงู„ุณู†ูŠู† ูˆุงู„ุญุณุงุจ ู…ุงุฎู„ู‚ ุงู„ู„ู‡ ุฐุงู„ูƒ ุงู„ุงุจุงู„ุญู‚ ูŠูุตู„ ุงู„ุขูŠุช ู„ู‚ูˆู… ูŠุนู„ู…ูˆู†ุŒ

Ilimin hai'at. Shine ilimin da ake sanin suffar taurari.
Da yanda suke fitowa. Sanin wannan ilimin yakan sa agane nahiyarda ake ciki.
Gabas koh yamma.
Kudu koh arewa.

ู‚ุงู„ ุงู„ู„ู‡ ุชุนุงู„ู‰ุŒ
ูˆุนู„ู…ุช ูˆุจุงู„ู†ุฌู… ู‡ู… ูŠู‡ุชุฏูˆู†ุŒ
ูˆู‚ุงู„ ุชุนุงู„ู‰ุŒ
ูˆู‡ูˆุงู„ุฐู‰ ุฌุนู„ ู„ูƒู… ุงู„ู†ุฌูˆู… ู„ุชู‡ุชุฏูˆุงุจู‡ุง ูู‰ ุธู„ู…ุช ุงู„ุจุฑ ูˆุงู„ุจุญุฑ ู‚ุฏ ูุตู„ู†ุง ุงู„ุขูŠุช ู„ู‚ูˆู… ูŠุนู„ู…ูˆู†ุŒ

ilmul tanjim shine iliminda ake sanin ษ—abi'ar taurari. Dacewarsu da rashin dacewarsu.
Sa'idi ne. Koh nahisi Koh mumtaziji.
Da wannan iliminne ake gane Sa'a Koh rashinta a abinda mutum zaiyi.๐Ÿ™

Misali koh fatauci zaka tafi wani gari Koh wata ฦ™asa.
Toh Yakamata kaduba kaje yankin da yadace da burujinka.
Toh zakafi samun Alkhairi Acan insha Allah.

Allah shine masani.

7 - 0

ILIMIN TAFIN HANNU TV CHANNEL
Posted 2 months ago

MASU HIKIMA SUNCE:

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Babbar hasara a lahira ita ce ka samu ladarka a cikin littafin wani ko ka samu zunubin wani a cikin littafinka. Kada ka zalunci mutane, kada ka shiga cikin hakkinsu. Idan ka yi haka za su washe ladarka ko su lafta ma zunubinsu.

*
*

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Masoyinka shi ne wanda yake kare ka idan aka aibata ka. Makiyinka a kullum fatar ya ke ka tozarta.

*
*

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Rayuwa takaitacciya ce. Kada ka cika ta da damuwa. Kada dogon guri ya dauke hankalinka daga mutuwa. Aikata alheri a kowane lokaci watakila shi zai zamo mabudin aljanna a gare ka.

*
*

๐Ÿ‘‰๐Ÿป Sau da yawa mu ke kuskuren fahimtar mutane. Ma'aunin da ba ya kuskure shi ne ka ajiye kanka a matsayin wanda kake wa hukunci.

3 - 0

ILIMIN TAFIN HANNU TV CHANNEL
Posted 2 months ago

Virgo Turabin 6 โ€“ daga 23 ga Agusta zuwa 22 ga Satumba)
---

Khalifson

4 - 0