Balangee TV wani sashe ne na Kamfanin Balangee Movie Tone, Kamfanin shirya Fina-finan Hausa da kuma Shirye-Shiryen Gidajen Talabijin A Ƙasar Hausa.
Wannan Channel Ɗin Zai dunga Kawo muku Shirye-shiryen Zamani Da kuma na Da, Wanda wasun mu Matasa da dama bamu sanshi ba. Haka zalika Zamu dunga Kawo muku Karantaccen Littafan Hausa wanda zasu dunga ɗebe maku kewa a kowani lokaci a duk inda kuke. Balangee TV zai kawo muku fina-finai da waƙoƙi daga Kannywood harda na mawakan zamani, bai kuma tsaya nan ba harda shirye shiryen girke girke, yadda ake kwalliya da kuma yadda Mace zata kula da mijinta. Ka zalika da damben Gargajiya in kuna biye damu a hankali duk zamu kawo maku su, baya ga haka zamu kawo maku hira ta musamman da Jama'ar gari akan wasu muhimman abubuwa wala Allah waɗanda zasu ba ku dariya ko wanda zaku ƙaru su. Farin cikin duk wanda suke tare damu shine namu.