WARURISM juyin juya hali ne na ruhi da tunani waɗanda aka tsara domin yaye ƙwaƙwanya da karkiyar da aka sakawa al'umma a cikin addini, siyasa, al'adu, da zamantakewa. Rukuni ne na ra'ayoyi, tunani, ƙa'idoji, da aƙidu domin ƴantar da al'umma daga ƙangin tunani, zalunci da bautar siyasa. Waɗannan aƙidu sun samo asali ne daga Ibrahim Abdullahi Warure, wato daga zurfin tunani na ilimi da hangen nesa waɗanda zasu yi jangora zuwa ga cikakken ƴanci da ɗaukakar ƙasa.