Salamu alaikum, Sunana Sumayya Abubakar, Kuma Ni yar jarida ce.
Barka da zuwa Tashar Youtube dina.
A wannan tashar, zan rinka kawo muku shirye-shirye masu nishadantarwa, ilimantarwa, da fadakarwa, musamman akan al’amuran yau da kullum da suka shafi rayuwar mu, duka a cikin harshen Hausa,
A cikin shiryen-shiryen wannan tashar tawa za mu rika tattataunawa tare da masu ruwa da tsaki: wato za a rika gayyato muku; Jarumai, Yan kasuwa, Mawaka, etc
Haka zalika tare da kawo muku Labaran gida da na waje, da kuma Hira da mutane daban-daban kan abubuwan dake faruwa na yau da kulum, Da dai sauran su
Kada kubari a baku labari
Saboda haka, ku danna SUBSCRIBE, kuma a danna kararrawa domin ku san duk lokacin da na daura sabon videyo.